Kenya: Raila Odinga zai kai kara kotu
August 17, 2022Sabon zababben shugaban Kenya William Ruto ya ce idan an kalubalanci sakamakon zabensa a kotu, a shirye yake ya halarci kotun domin kare nasarar da ya samu. Wannan na zuwa ne a yayin da kasar mafi kwanciyar hankali a gabashin Afirka ke dakon yiwuwar daukaka kara daga dan takarar da ya sha kaye Raila Odinga.
Ruto wanda ya yi jawabi ga 'yan jarida bayan ganawa da kawancen 'yan siyasar da suka mara masa baya, ya ce gwamnatinsa ba za ta saurari kutungwila ko barazana ba kamar yadda aka gani, yana mai cewa sun mayar da hankalinsu ne kan dawo da martabar kasar. Ruto wanda shi ne mataimakin shugaban kasar a ranar litinin da ta gabata aka bayyyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a makon da ya wuce, sai dai an sami rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan hukumar zaben gabanin baiyana sakamakon.
Karo na biyar ke nan da Odinga yake takarar shugaban kasa. Babu tabbas a game da hujjojin da yake so ya gabatar na kalubalantar zaben da 'yan kasar Kenya da dama da masu sa ido suka ce ya gudana lami lafiya cikin tsafta. Sai dai Raila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar, yana mai cewa an yi rashin gaskiyya tare da shan alwashin bin duk wani zabin doka da ya dace.