Rahoton hukumar UNESCO a game da illimi a dunia
November 10, 2005Jiya ne hukumar Majalisar Dinkin Dunia mai kulla da ilimi da al´adu, wato UNESCO, ta bayyana rahoton ta, na 4, a game da illimi a dunia baki daya.
Rahoton ya ce dattawa million 771 ne a fadin dunia basu iya karatu ba da rubutu na boko.
A kasashe kamar su Ethiopia Bengladesh, Ghana, Nepal da Mozambik kashi 63 bisa 100 na dattawa na fama da duhun jahilci.
Kazalika a kasashe irin su Mali, Niger, da Burkina Faso, kasa ga kashi 13 bisa 100 kaccal na ,dattawan kasar su ka samu illimin yaki da jahilci.
Mafi yawan masu fama da karancin illimin sun fito daga jansin mata.
Rahoton ya nunar da cewa matsalolin talauci na kara raddadin jahilcin.
A bangaren matasa yan tsakanin shekaru 15 zuwa 25 da aihuwa su million 132 ne a dunia ke cikin duhu, mafi yawan su a kasashe matalauta.