Rabuwar kawuna kan siyasar Putin a Rasha
February 28, 2020Talla
Sakamakon binciken da kamfanin ya gudanar a kwana-kwanan ya nuna cewa kaso 46 cikin 100 na mutanen kasar sun nuna sha'awarsu ta Shugaba Putin ya ci gaba da rike madafun iko bayan ya kammala wa'adinsa. Yayin da kaso 45 suka nuna cewa a kai kasuwa. Shugaba Putin mai shekaru 67 ya yi wurin shekaru 20 yana mulkin kasar Rasha kuma shi ne shugaban da ya fi dadewa a kan karaga tun bayan gwamnatin Joseph Stalin.
Nan da wata biyu ne dai ake sa ran 'yan kasar za su gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a a kan wani gyaran tsarin mulki, kuma idan har aka yi wannan gyaran, ana ganin gwamnatin Putin za ta samu damar fakewa da gyaran wurin ci gaba da darewa a madafun iko.