1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi sun bambanta kan kama makamai a Niamey

Gazali Abdou Tasawa MAB
February 23, 2024

Hukumomin tsaron Nijar sun sanar da kama tarin makamai da harsasai a wani samame da suka kai a cibiyar rundunar tsaro ta Turai wato Eucap-Sahel , inda suka ce wani jami’in sojan Faransa ne ya shigo da su daga Agadez.

https://p.dw.com/p/4cnvC
Sojojin Nijar na shan yabo daga 'yan kasa a lokacin da suka yi yunkuri kan Faransa
Sojojin Nijar na shan yabo daga 'yan kasa a lokacin da suka yi yunkuri kan Faransa Hoto: AFP/Getty Images

Sanarwar ma'aikatar tsaron Nijar ta fitar ta bayyana cewa samamen da jami'an tsaro na jendarma da kuma 'yan sanda suka kai a cibiyardakarun EUCAP-SAHEL da kuma wani gida inda jam'in sojin Faransa suka yi zaman haya kafin korar su daga Nijar, ya ba su damar kama tarin makaman yaki da suka hada da jirage maras matuka guda hudu da bindigo manya sanfarin Oberland guda 20, da kanana bindigogi na hannu masu sarrafa kansu guda 27 da harsasai manya da kanana kusan dubu 150, da gurneti 53,da bindigogi harba rokoki, da motoci sanfarin 4*4 wasunsu dauke da lambobin boge da tabarau hangen nesa na bindiga guda 56 da riguna masu sulke 170 da hular kwano 11 , da wayar tafi da gidanka da sauran kayan yaki daban-daban.

Karin bayani:Sabon kawancen tsaro na Sahel zai fuskanci kalubale

A shekarun baya, an samu kyakkyawar hadin kai tsakanin sojojin Nijar da na Faransa
A shekarun baya, an samu kyakkyawar hadin kai tsakanin sojojin Nijar da na FaransaHoto: ALAIN JOCARD/AFP/Getty Images

A yayin da yake tsokaci kan wannan kame Bana Ibrahim, dan fafutika mai goyon bayan mulkin sojan Nijar  ya ce wannan na kara nuni da cewa har yanzu akwai barazanar harin Faransakan Nijar. A bangarensa,Siraji Issa na Kungiyar Mojen cewa ya yi hukumomin mulkin sojan Nijar sun kirkiro da wannan shiri ne kawai don dauke hankalin al'umma daga jerin matsalolin da suke fuskanta, wadanda sojojin suka kasa shawo kansu. Sai dai wasu 'yan Nijar na ganin cewar akwai bukatar yin cikakken bincike a wannan lamari kafin zargin Faransar da neman amfani da rundunar ta EUCAP-SAHEL wajen shirya wata makarkashiya ga Nijar, kamar yadda Soule Oumarou na kungiyar FCR ya bayyana.

Karin bayani: Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar

Jama'a sun kashe kunne don jin amsar da rundunar tsaron ta  KungiyarTarayyar Turai EU a Sahel wato Eucap-Sahel da ma kasar Faransa za su bayar a game da wannan zargi mai karfi da hukumomin mulkin sojin Nijar din suka yi masu.