Pyongyang za ta fuskanci sabon takunkumi
September 12, 2017Manyan kasashe da ke kawance da Amirka a yankin Asiya a ranar Talata sun yi lale marhabun da shirin Majalisar Dinkin Duniya na kara yawan takunkumi da za a kakaba wa Koriya ta Arewa ciki har da batun hana fitar da kayayyakin da ake sakawa a kasar don sayarwa a ketare, abin da ke zuwa bayan gwajin makamin nukiliya a karo na shida.
Kasar Japan da Koriya ta Kudu bayan gabatar da wannan kudiri da Amirka ta yi ga kwamitin sulhu na MDD, sun bayyana cewa a shirye suke wajen kara yawan takunkumi ga mahukuntan na birnin Pyongyang ganin yadda suke kunnen kashi duk da gargadin da ake musu kan shirinsu na hada makaman kare dangi.
Matakin da aka cimma na ranar Litinin shi ne karo na tara da mambobin kwamitin sulhu 15 suka amince da shi tun daga shekarar 2006 kan Koriya ta Arewa mai kudiri na mallakar makamai masu linzami da makamin nukiliya.