Putin yayi rantsuwar kama aiki
May 7, 2012A wannan Litinin a birnin Mosko aka yi bikin rantsar da tsohon Firaministan Rasha Vladimir Putin a muƙamin sabon shugaban ƙasa. Putin mai shekaru 59 a duniya shi ne shugaban Rasha na farko tun bayan rugujewar Tarayyar Rasha da zai yi wa'adin shugabanci na shekaru shida, kuma yayi alƙawarin kare tsarin mulki na demokraɗiyya yana mai cewa:
"Zan yi iya ƙoƙarin kare wannan yarda da miliyoyin 'yan ƙasar Rasha suka nuna mini. Dimitry Medvedev ya yi nasarar kawo ƙarshen wa'adin mulkinsa na shekaru huɗu. Shugabancinsa ya taka rawa wajen sabunta wannan ƙasa. Shekaru masu zuwa za su kasance masu muhimmanci ga makomar Rasha. Za mu cimma burinmu idan muka zama tsintsaya maɗaurinki ɗaya."
A ranar Lahadi an kame mutane 450 ciki har da ƙusoshin 'yan adawa da suka yi zanga-zangar yin tir da Putin a birnin Mosko. Putin dai ya taɓa riƙe muƙamin shugaban Rasha daga shekarar 2000 zuwa 2008.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamdou Awal Balarabe