1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya ja hankalin Yamma kan Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
January 19, 2023

Kasar Rasha ta yi gargadin cewa matakin da kasashen yammacin duniya ke niyar dauka na kai wa Ukraine makamai masu cin dogon zango zai iya tsananta rikici tsakanin kyiv da Moscow.

https://p.dw.com/p/4MQOM
Shugaba Vladimir Putin na kasar RashaHoto: Aleksey Babushkin/Sputnik Kremlin/AP/dpa/picture alliance

kakakin fadar mulki ta Kremlin Dmitry Peskov ne ya yi wannan bayani, inda ya ce Rasha ba za ta lamunta da faduwar maki a wani yanki na kasarta ba tare da mayar da martani da ya dace ba. Wannan kalamin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki matakin Jamus na jan kafa wajen mika masa manyan tankunan yaki, a jajibirin wani muhimmin taro na kungiyar tuntuba ta Ukraine a birnin Ramstein na Jamus, domin daidaita ci gaban agaji a Kyiv. Duk da cewa tun farkon yakin dai,

kasashen Yamma sun ki kai makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa birnin kyiv, amma Moscow ta zargi sojojin Ukraine da kai hare-hare da jirage marasa matuka a yankin Crimea.