1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin na ganawa da Erdogan na Turkiyya

Muntaqa AhiwaDecember 1, 2014

Putin na Rasha na ganawa da takwaransa Erdogan, na Turkiyya amma bacin cewa batun farashin iskar gas ya mamaye tattaunawarsu, kasashen yamma na shakku

https://p.dw.com/p/1Dxmt
Putin bei Erdogan 01.12.2014
Hoto: Reuters/U. Bektas

Ranar litini (01.12.2014) , shugaba Reccep Tayyib Erdogan na kasar Turkiyya, ya karbi bakuncin takwaran sa na Rasha Vladimir Putin, a wani kokari na karfafa dangantaka tsakanin kasashen, wadanda a baya suka sha takaddama kan rikicin kasashen Syria dama na Ukraine.

Ganawar da ta kasance a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, daga cikin batutuwan da ke kan gaba a wannan ziyara, shugabannin biyu, suna tattauna batun harkokin makamashi ganin bukatar saukin farashin gas da Turkiyya ke bukata dama kara yawan sa, gami da wasu muhimman batutuwa na diplomasiyya.

Kasar Rasha da kasashen yamma suka maida ita saniyar ware saboda rikicin Ukraine, na kokarin kyautata dangantaka ne da Turkiyyan, musamman ma ganin yadda Turkiyyar ce za ta karbi bakwancin taron koli na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G20.