Rasha za ta mayarwa Amirka martani
August 23, 2019Talla
Shugaban ya ce ya umarci ministan tsaron kasar da ya nazarci irin barazanar da harba rokar ta Amirka kan iya yi, kafin daukar duk wasu matakai a yayin da yake jagorantar wani taron koli na harkokin tsaron kasar.
Tun daga farko dai kasashen China da Rasha sun soki lamirim matakin na kasar Amirka da ke zaman irinsa na farko tun bayan kawo karshen yakin cacar baka, tare da bayyana shi a matsayin wata barazanar da ke iya maida hannun agogo baya, kana kuma hakan na iya harzuka kasashe shiga riganganton kerwa manyan makamai.