1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pretoria za ta kare kai a ICC kan al-Bashir

Yusuf Bala Nayaya
April 7, 2017

Mahukuntan a Afirka ta Kudu dai na da kalubale a gabansu na kare kai bayan rashin mutunta umarnin kotun da suke gaba wajen ganin an kafata, lokacin da Shugaba al-Bashir ya kubuce mata a wata ziyara.

https://p.dw.com/p/2aqKx
Omar al-Bashir in Sudan
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Ali

A ranar Juma'an nan ce kasar Afirka ta Kudu za ta kare kanta a gaban alkalan kotun da ke hukunta masu manyan laifuka ta ICC saboda rashin kama Shugaba Omar al-Bashir na Sudan lokacin da ya kai wata ziyara a kasar.

Mahukuntan na birnin Pretoria dai na da kalubale a gabansu na kare kai bayan rashin mutunta umarnin kotun da suke gaba wajen ganin an kafata.

Masu gabatar da kara dai a kotun ta ICC na cike da fushin ci gaba da kasancewar al-Bashir bisa mulki duk da sanya sammaci na kasa da kasa a kansa a shekarar 2009 da 2010.

Ana dai tuhumarsa da laifuka 10 uku daga ciki na aikata kisan kiyashi da laifin yaki a yankin Dafur da ya yi sanadi na rayukan mutane 300,000 da sanya sama da miliyan biyu kauracewa muhallansu kamar yadda MDD ta nunar.