1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 75 da balle sansanin Auschwitz

Gazali Abdou Tasawa
January 27, 2020

Shekaru 75 ke nan da 'yanto mutanen da aka tsare a sansanin gwale-gwale na Auschwitz da ke kasar Poland da 'yan Nazi suka samar. Sojojin Tarayyar Soviet ne dai suka ceto mutanen da aka tsare a sansanin

https://p.dw.com/p/3Wr2R
Polen Gedenken l Das Konzentrationslager Auschwitz, 75. Jahrestag der Befreiung l u.a. Ronald Steven Lauder
Hoto: DW/P. Kouparanis

Gwamnatin 'yan Nazi ta Adolph Hitler da ke mulki a Jamus a wancan lokaci ne dai, ta azabtar tare da halaka mutane sama da miliyan daya akasarinsu Yahudawa a loakcin yakin duniya na biyu.

Albarkacin wannan rana mutane sama da 200 daga cikin fursinonin da aka tsare a sansanin na Auschwitz wadanda suka tsira da rayukansu da kuma ke raye, za su halarci bikin domin bayar da shaida kan yadda rayuwa ta kasance a sansanin gwale-gwalen a wancen lokaci da nufin fadakar da duniya, a daidai lokacin da akidar kyamar Yahudawa da ma kai masu farmaki ke karuwa musamman a kasashen Turai da Amirka.

Shugabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin 60 ake sa ran za su halarci bikin na wannan rana na birnin Auschwitz.