Peres na goyon bayan Herzog a Isra'ila
March 12, 2015Talla
Tsohon shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres ya fito fili ya nuna goyon baya ga dan takarar jami'iyyar Labour Isaac Herzog wanda zai kalubalanci firaminista Benjamin Netanyahu a zaben 'yan majalisa da zai gudana a ranar 17 ga watan Maris 2015.
Cikin wata sanarwa da ya fitar Peres ya ce ya san Herzog tun da jimawa, sannan ya ga kamun ludayinsa da kuma rawar da ya taka wajen ciyar da Isra'ila gaba. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya-bayannan ta nunar da cewa dan takara Isaac Herzog ya na gaban firaminista mai barin gado Benjamin Netanyahu.
Shimon Peres da ya sauka daga mukamin shugaban kasa a watan Yulin bara, ya na daga cikin wadanda suke sukar manufofin firaminista Benjamin Netanyahu.