1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP za ta gudanar da binciken zargin cin hanci

Uwais Abubakar Idris/ Zainab Mohammed AbubakarMay 5, 2015

Jam'iyyar ta kadamar da kwamitin da zai bincika tare da yunkurin farfado da martabarta bayan shan kaye a zaben shugaban kasa daura da matsalolin cikin gida .

https://p.dw.com/p/1FKay
Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Hoto: DW/U.Musa

To ana dai yin wawaso na milyoyin naira ne a jamiyyar ta PDP inda manyan jami'anta suka yi wadaka da rabawa kansu kudadden daga naira bilyan 10 da jam'iyyar ta samu a matsayin kudaden sayar da takardun shiga takara a zaben da jam'iyyar ta sha mumunan kaye irinsa na farko a shekaru 16 na wanzuwarta.

Zargin sama da fadin da a yanzu ya sanya jamiyyar fuskantar gaza biyan albashi da ma alawus-alawus ga ma'aikata ya sanya tada jijiyar wuya tare ma da kafa kwamiti don ya binciko gaskiyar abinda ya faru domin gyara . Alh Adamu Maina Waziri dan kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP shi ne mukaddashin sakataren wannan kwamiti.

"Idan kana son ka jefo fitina a wannan zamani a kasarmu ta Najeriya to kawo maganar kudi. Wannan abin da muke yi a akwai bincike na gilla akwai kuma bincike na neman mafita. Mu zamu maida hankali mu yi bincike mu yi aiki don mu fiyar da jamiyyarmu daga halin da muka shiga wanda bamu so amma kuma Allah ya samu a ciki. Mu muna ganin ba maganar kudi ba ne maganar ta wuce kudi''.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Zargin sama da fadi da kudadden jam'iyya na kara jefa PDP cikin mawuyacin hali na kokarin gyara cikin gida bayan waje ya barke, doming wasu jami'an jamiyyar na masu nuna 'yar yatsa ga abinda ya faru da cewa in ba gaskiya ba ne to kamata ya yi su nufi kotu. Barista Abdullahi Jalo shi ne mataimakin sakataren yada labaru na jam'iyyar .

‘'A nan abinda hankali zai kama shi ne ga kudi milyan 250 shugabanin gudanarwar jam'iyya sun raba wa kansu. Kai ba'a baka naka ba kenan… A'a ai ina jiran a nuna min cewa kai Barista Jalo an baka kaza. Ina ce an kafa kwamiti gyara ne ya hada da biciken zargin da aka yi. Ana maganr jam'iyar PDP zata zama jam'iyya mai karfi ta adawa, ita kuwa adawa ai bata yiwuwa sai da gaskiya. Mai buni a gidansa ai baya zuwa kashe gobara''.

Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Jiga jigan jam'iyyar PDPHoto: DW/U.Musa

Bullar zargin cin hanci da rashawa a cikin jam'iyyar a dai dai lokacin da ta kafa kwamitin da zai duba abubuwan da suka faru da ya sanya jam'iyyar shan kaye a zaben shugaban kasar da aka kammala a kasar na zama jan aiki da ke gaban 'yan kwamitin.

An dai yi taron ba tare da shugaban jam'iyyar Ahmed Adamu Muazu ba, wanda tuni ake takaddama a kan shugabancin jam'iyyar nasa, baya ga zargin batar dabon da milyoyin nairori na jam'iyyar suka yi. Kokarin shawo kan batun a cikin gida ya sanya shugaban kasar Goodluck hana wa duk wani dan jam'iyyar sake suka a kan batutuwan da suka faru.