PDP: Rikicin shugabanci na kara tsanani
June 14, 2016A wannan Talatar (14.06.2016) ce dai Ali Madu Sharif ya hedikwatar jam'iyyar ta PDP inda ya dage cewar shi ne hallastaccen shugaban jamiyyar ta PDP, abun kuma da ya sake dagula rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta ta bangaren shugabanci. Sharif din dai ya bijirewa kokarin da ake yi na kawar da shi daga kan kujerar jagorancin jam'iyyar duk kuwa da matsayin da gwamnonin jam'iyyar suka dauka na juya masa baya.
Sai dai duk da irin kalubale da adawa da Sharif din ke fuskanta, wakilin DW Abuja Ubale Musa ya iske ya na tafi da harkokinsa cikin gidan na Wadata. Tuni dai bangaren Ahmed Mohammed Makarfi ya ce wannan mataki na shiga gidan na Wadata da Sharif din ya yi ba zai razana shi don kuwa ragama ta jagorantar jam'iyyar na hannunsa.
Ana dai yi wa wannan takun saka tsakanin mutane biyu da ke ikirari kasancewa shugabanin jam'iyyar kallon wata hanya da za ta iya rusa jam'iyyar duk kuwa da kokarin da jiga-jiganta suka ce suna yi wajen warware matsalolin da ke addabarta. Wani dan jam'iyyar mai suna Aminu Yakudima ya shaida shaidawa DW cewar dattawan jam'iyyar za su iya kawo karshen komai cikin kankanin lokaci