1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na fiskantar shan kaye a majalisar Tarayya

April 10, 2011

Sakamakon farko na zaɓen 'yan majalisar wakilai da na dattijai da aka yi jiya a Najeriya, ya nuna alamun samun sauyi a majalisar.

https://p.dw.com/p/RGqv
Masu zaɓe a KanoHoto: DW

A Tarrayar Najeriya an fara samun sakamakon zaɓen 'yan majalisun ƙasar wanda ya gudana a jiya. Inda alamu ke nuna cewa jam'iyyar PDP dake mulkin ƙasar tun shekaru sha biyu, ta na fiskantar shan kaye a majalisar dokokin ƙasar. Rohotannin da jaridun ƙasar suka ruwaito wadanda hukuma ba ta kai ga bayyanawa, sunce ƙusoshin PDP waɗanda suka haɗa da Shugaba Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo, Da kakakin Majalisar doki Bankole, da kuma Obasanjo, haɗe da gwamnan Jahar Katsina duk ba su ci rumfunan zaɓensu ba.

Sakamakon wucin gadi wanda ba na hukuma ba

Parlamentswahl 2011 in Kano State Nigeria
Wani Malami ke kaɗa ƙuri'a a KanoHoto: DW

Rahotannin suka ce a mazaɓu biyu na cikin fadar shugaban ƙasa da VIlla, Jam'iyyar Buhari ce taci, inda a ɗaya rumfar CPC ta lashe ƙuri'u 300, yayin da PDP ta samu 15. Kazalika Shima shugaban tsohon shugaba Obansanjo, a rumfarsa ACN ce taci, inda jahar ta sa ɗiyarsa Iyabo Bello da kuma kakakin majalisar Tarrayar Bankole duk sun sha ƙasa a zaɓen na jiya. Kazalika a ƙatsina PDP ta sha kaye a mazaɓar fadar gwamnatin jahar, inda jam'iyyar Buhari ta ci. Kazalika kawo yanzu alamu sun nuna cewa jam'iyyar PDP tasha kaye a jahar Zamfara, inda jam'iyyar ANPP ke da gagarumin rinjaye a zaɓen, aksarin sakamokon farko daga yan kudu maso yammaci, ya nuna cewa jam'iyar ACN ce ke kan gaba. Shi ma gwamnan Kano ance bai ci rumfar da ya kaɗa ƙuri'a ba da kuama rumfar gidan gwamnatin jahar Kano, inda duk CPC ta lashe. a Jahar Kaduna rahotanni sukace CPC ta yiwa PDP fintinkau. Sai dai a jahar Jigawa kawo yanzu PDP ce ke kan gaba yayinda ake ci gaba da samun saka mako.

Amma duka waɗannan sakamkon sai hukumar zaɓe wato INEC ta tabbatar da su tukuna.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi