PDP na cikin hali na tsaka mai wuya
June 19, 2013Wannan na faruwa ne a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da taron kwamitin zartarwar jam'iyyar da ma karuwar barakar da ke tsakanin gwamnonmin jam'iyyar ke karuwa.
An dai ja daga tare ma da jan layi a kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar ta PDP mai mulkin Najeriya da sannu a hankali ya kama hanyar lakume wasu jiga-jigan jam'iyyar da wani bangare na gwamnoninta ke ganin ba'a yi masu ta dadi ba kuma ba za su yarda ba.
Takun sakar da aka dade ana fuskanta tsakanin wasu gwamnonin Najeriyar da shugaban jam'iyyar ta PDP da wasu majiyoyi suka bayyana cewa kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa ya bukace shi da ya sauka daga mukamminsa, abin da shugaban jam'iyyar ya ce ba zata sabu ba kuma ba zai sauka ba.
Ya ce "in sauka zuwa ina? Na hau kan wannan mukami ne in jagoranci jam'iyyar PDP ina nan kan mukamin nan daram dam".
To sai dai ga Alahaji Isa Tafida Mafindi wakili a kwamitin zatarwar jam'iyyar wanda suka yi taro a kan wannan batu cewa ya yi duk ba ma haka maganar take ba.
Ya ce "babu wanda yace kowa ya sauka, wadanda suka sauka su ne mutane takwas da suka hada da sakataren tsare-tsare da sakatare na kasa da hade da mutum guda wanda kotu ta cire, shi ne sakatare na kasa. Shugaban jam'iyya Bamanga Tukur hukumar zabe ta ce zabensa dai dai aka yi, ba'a kai shi gaban kwamitin ladabtarwa ba, don haka wa zai ce ya sauka? A kan me! To fa iyakan labarin kenan, mutane suke ta ruruta magana wannan ya sauka wannan ya sauka sai kace babu wanda ya kafa su".
A yayin da kurar rikicin jam'iyyar ta PDP ke kara tirnikewa musamman saboda yadda gwanoninta da a can baya a kan sansu a matsayin tsintsiya madaurinki daya, a yanzu suka dare gida biyu da masu goyon bayan gwaman Jonah Jang na jihar Plateu da Rotimi Amaechi na Rivers, abin da ya sanya kallon jamiyyar a matsayin wacce ke neman lakume 'yayanta. Dr Rabe Nasiri dan jam'iyyar PDP da ya bayyana yadda yake kalon lamarin.
"To na farko dai ina son mutane su gane cewa ban yi mamaki ba saboda PDP jam'iyya ce wadda take taka kidin rawar mutum daya, dama can haka suke yi. Kuma duk wanda yake cikin jamiyyar PDP ya kasance a cikinta ne don yana samun abin da yake samu, kuma mu da muke cikin PDP muna nan muna kara auna sikelinmu mu duba in abin zai gyaru. Don haka magana ce ta Najeriya magana ce ta rike abin da ya kamata, magana ce ta rike amanar Najeriya da ci gaba".
A bin jira a gani shine irin wairnar da za'a toya a taron kwamitin zartarwar jam'iyyar da za'a gudanar a ranar alhamis din inda zata ware ko ta waraye a rigimar da zata yi awon gaba da shugabanin jam'iyyar da dama da hukumar zaben Najeriya ta ja dagar cewar ba'a fa yi zabensu ba nada su aka yi, kuma ya sabawa tsarin demokradiyya.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar