1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya bukaci mataki kan sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
October 29, 2021

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis a wata sanarwa da ya fitar gabanin babban taron duniya kan sauyin yanayi COP26 yace wajibi ne shugabanni su dauki matakan gaggawa don shawo kan dumamar duniya.

https://p.dw.com/p/42KN1
Vatikan Besuch vom Vizepräsident Joe Biden beim Papst Franziskus (2016)
Hoto: Evandro Inetti/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Paparoman na shirin karbar bakuncin shugaban Amirka Joe Biden tare da mai dakinsa Jill a fadar Vatican.

Za su tattauna batutuwa da suka shafi yaki da annobar Corona da sauyin yanayi da kuma yaki da talauci a duniya.

Daga bisani Biden zai kuma gana da jami'an gwamnatin Italiya da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Wannan dai ita ce ziyarar Biden ta biyu zuwa kasashen waje tun bayan da ya hau karagar mulki. Ana kuma sa ran zai halarci taron sauyin yanayi na duniya COP26 ranar Litinin a Glasgow Scotland.