OXFAM ta ce 'yan gudun hijiran Siriya na cikin wahala
May 20, 2013Talla
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta bayyana ta ce zafin da ake yi wanda ya zarta sama da degre 40 a maunin Celisius. Ya sa tuni da wasu cututtuka suka fara ɓula a jikin yan gudun hijirar,irinsu ƙuraje da gudawa dai wasu cututukan da suka shahi fata.
Ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya da suka kawo mata ɗauki, domin ci gaba da yin aikin samar da ruwan sha mai tsafta da abinci da kuma magunguna ga 'yan gudun hijrar da ke jibge a cikin sansanonnin wucin gadi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman