SiyasaAfirka
Zimbabwe na samun karuwar masu Covid-19
December 3, 2021Talla
Ministan lafayar kasar Constantino Chiwenga ya ce Zimbabwe na cikin yanayi mai hatsari a kan batun corona. Rahotannin da ke shigo mana yanzu-yanzun nan na cewa Zimbabwen ta samu masu dauke da corona samfurin Omicron guda 5o kawo yammacin wannan Jumma'a.
Kasar dai na cikin kasashen kudancin Afirka da manyan kasashen duniya suka yanke sufurin sama a tsakaninsu da su biyo bayan bullar da Omicron mai ban tsoro ya yi a Afirka ta Kudu. Sai dai hukumomin Zimbabwe sun kakaba sabbin dokoki masu tsauri don shawo kan lamarin.