Obama ya samu lambar yabo ta Nobel
October 9, 2009A ranar juma'ar nan ne kwamitin dake bada kyautan Nobel ta Duniya dake Norway ta sanar da sunan shugaban Amirka Barak Obama a matsayin wanda ya lashe kyautan Nobel na zaman lafiya na wannan shekara. Kwamitin ta bada wannan kyautan zaman lafiya ne bisa ƙoƙarin da shugaban na Amirka yake takawa wajen samar da zaman lafiya a Duniya baki ɗaya.
Shugaban kwamitin dake bada kyautan Nobel na zaman lafiya kenan Thorbjörn Jaglang yake sanar da kyautan Nobel na zaman lafiya na wannan shekara ga shugaba Obama.
Wannan sanarwa da kwamitin dake da mazaunin sa a ƙasar Norway ya fitar yazo ne da ba zata ga jama'a da dama, bawai don ana ganin shugaba Obaman bai cancanci samun kyautanr ba, a'a sai don ganin wannan shine karon farko da ake baiwa wani shugaban ƙasa da bai daɗe akan karagar mulki, irin wannan kyauta na zaman lafiya ba. Yan kwamitin na Nobel dai sun kare wannan matsayin na ba da wannan kyauta ga shugaba Obama da suka haɗa da ƙoƙarin da yakeyi baji ba gani wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma hana yaɗuwan makamai masu guba a duniya baki ɗaya.shugaban kwamitin Thobjörn Jagland yaci gaba da cewar
" idan kuka duba tarihin wannan kyautan na zaman lafiya,ako yaushe muna ƙoƙarin karfafa guiwan abin kirki ne da wasu al'uma ko wani keyi. Misali a lokacin da Willy Brandt ya samu wannan kyauta a shekarar 1970 da abinda ya biyo baya a tarayyar turai da kuma Michail Gorbatschow na tsohuwar ƙasar Rasha da shima ya samu wannan kyauta, sai yanzu kuma shugaba obama, wanda ke ƙoƙarin bunƙasa hanyoyin diflomasiya ta anfani da kafofi irin su Majalisar Ɗunkin Duniya".
Shi dai shugaba Obama ɗan shekaru 48 da haihuwa ya zama shugaban Amurka baƙar fata na farko ne a ranar ashirin ga watan janairun bana, kuma tun bayan hawan sa mulki ya ɗauki matakai da suka haɗa na janye sojojin Amirka daga Iraƙi da batun rage ɗumamar yanayi a duniya, haka kuma shine shugaban Amurka baƙar fata na farko daya shirya taron shugabanin Isra'ila dana Falasɗinawa da kuma buɗe sabon shafin tattaunawa na Difulomasiya da ƙasashen Iran da Bama da kuma Koriya ta arewa, akan shirin su na Nukiliya da Demokiraɗiya.
Ga Duniyar musulmi kuma Shugaban Obaman ya buɗe sabon babin tattaunawa tare da fahimtar juna tsakanin Amurka da Turai da kuma musulmi kamar yadda ya jaddada a wannan jawabi daya gabatar a birnin Kairo ta ƙasar Masar a wannan shekara.
Tuni dai shugabanin Duniya irinsu Angela Merkel na Jamus da Nikolas Sarkozy na Faransa da Karzai na Afghanista suka yaba da sanarwar bada kyautar ta Nobel na zaman lafiyan na bana ga Shugaba Barack Hussain Obama na Amurka.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Umaru Aliyu