1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Amirka ya ce tilas a dakile ayyukan 'yan ta'adda

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 13, 2016

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce ba za a iya kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda masu kaifin kishin addini da suka addabi duniya ta hanyar daukar tsauraran matakai na fushi a kansu ba.

https://p.dw.com/p/1HcFG
Shugaba Barack Obama na Amirka
Shugaba Barack Obama na AmirkaHoto: picture-alliance/dpa/E. Vucci

Obama ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabinsa na bakwai kuma na karshe a matsayin shugaban kasa a gaban majalisar dokokin kasar. Ya kara da cewa sun dauki yakin da suke da kungiyar 'yan ta'addan IS tamkar yakin duniya na uku, a yayin da mayakan ke hallaka rayukan al'umma wanda ya zamo wajibi a dakatar da ayyukansu.

Ya ce: "Mayaka masu yawa na makare bayan mayan motoci kirar pickup, kuma suna daukar rayukan mutane a gidaje da guraren taruwar jama'a, sun kasance babbar barazana ga rayuwar fararen hula. Tilas ne a dakatar da su."