1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya bayyana manufofinsa na yaƙi da Ebola

Abdourahamane HassaneSeptember 17, 2014

Amirka ta ce za ta aike da sojoji dubu uku zuwa ƙasashen yammacin Afirka domin daƙile cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/1DDiS
NATO Gipfel in Wales 05.09.2014
Hoto: Reuters/Yves Herman

Shirin wanda shugaba Barack Obama ya bayyana a jiya daga cibiyar yaƙi da cutar ta Ebola a Atlanta da ke a yankin kudu maso gabashi na Amirka.

Ya ce cutar babbar barazana ce ga duniya baki daya.'' Cuta ce da aka gaza murƙusheta tana yaɗuwa da sauri kamar wutar daji, a yau miliyoyin jama'a na fama da ita a yammancin Afirka,kuma idan ba a yi wani yunƙurin daƙileta ba wasu ƙarin jama'ar za su iya kamuwa. Sojojin na Amirka da za a tura a cikin ƙasashen na Afirka za su gina sabbin asibitoci domin jinyar masu larurar ta Ebola.