1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar za ta bude sabon sansanin soji

Ramatu Garba Baba
August 6, 2021

Fadar gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta sanar da shirin kafa sabon sansanin soji don yakar 'yan ta'addan da hare-harensu suka hana zaman lafiya da kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/3yeqM
Symbolbild Afrika Sicherheit im Sahel
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta shirya girka wani sabon sansanin soji a yankin Kudu maso Gabashin kasar mai fama da aiyukan 'yan ta'adda. Fadar gwamnatin kasar ce ta sanar da hakan a wannan Juma'ar a kokarin da gwamnatin ta ce, tana yi don magance matsalar tsaro, sansanin mai suna BA 501, zai kasance mai nisan kilomita talatin da biyu daga jahar Diffa, daya daga cikin yankunan kasar da ya fuskanci munanan hare-haren mayakan Boko Haram. 

Baya ga Boko Haram, Nijar na fuskantar kalubalen tsaro daga mayakan jihadi na kasar Mali reshen IS da Al Qaeda. 'Yan gudun hijira kusan dubu dari uku ne yanzu haka ke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijirar Jahar Diffa, sun hade da wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa daga gidajensu a Najeriyar da ke makwabtaka da jamhuriyyar Nijar.