Nijar: 'Yan adawa sun janye daga shiga zabe
March 9, 2016Hadin gwiwar jam'iyyun adawa na COPA sun yi kira ga magoya bayansu da su fice daga wakilicin da suke a hukumar zabe tun daga mataki na kasa har ya zuwa na kananan hukumomi.
Wannan mataki na 'yan adawar ya sanya shugaban kasar Isoufou Mahamadou wanda tuni ya fara yakin neman zabe cikin wani yanayi mai sarkakiya.
'Yan adawan na Nijar dai sun soki lamirin yadda shugaban kasar ke tafiyar da lamarin, inda suka ce yana son cigaba da mulki ne ko ta halin kaka ba tare da yin biyayya ga dokokin kasa ba, bayan da suka zargi bangaran na gwamnati da tafka magudi a zaben da ya gudana zagaye na farko, zagin da bangaran gwamnatin ya musanta inda ya ce zaben ya gudana cikin haske.
Tuni dai masu lura da al'ammuran siyasar ta Nijar na ganin cewa kasar na daf da fada cikin wani hali na rishin tabbas muddin zaben bai gudana cikin sulhu ba.