Turai za ta taimakawa Nijar da kudi
May 26, 2022Kimanin kudade miliyan dubu 70 na CFA ne dai kungiyar tarayyar Turai za ta saka a kasar ta Nijar, inda suka kasu kashi uku, wanda kashi na farko zai duba batun samar da muradun gwamnati a yankin da ake kira na iyakoki uku inda Nijar din ke makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso, inda lamura suka tabarbare sosai.
Babu asibitoci babu makarantu duk sun rufe sannan da kasancewar ita kanta hukuma a wasu yankunan kasar inda 'yan ta’adda ke cin karensu babu babbaka. Da take magana kan wannan batu, wakiliyar kungiyar ta tarayyar Turai a kasar ta Nijar Denisa Elena Ionete, ta ce rattaba hannu kan wannan yarjejeniyoyi na nuni da amintakar da ke tsakanin kasar ta Nijar da kungiyar ta Tarayyar Turai:
"Akwai batun harkokin ilimi da bayar da horo, da samar da ayyukan yi da taimaka wa kananan hukumomi domin su gudanar da ayyukansu na gwamnati a wadannan yankuna na iyakoki uku inda Nijar ke makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso, sannan akwai batun inganta harkokin diflomasiyya tsakanin Nijar da Tarayyar Turai. Wannan rattaba hannu da muka yi wani ma’auni ne da ke nuna kyaukyawar dangantakar da ke tsakanin kasar Nijar da Tarayyar Turai, kuma hakan zai bamu damar ka iwa ga wasu tarin tsare-tsare masu mahimmanci da Tarayyar Turai za ta samar a kasar ta Nijar".
Saka hannu kan wadannan yarjejeniyoyi dai na zuwa ne wata daya bayan wata ziyara da kwamishiniyar Tarayyar Turai mai kula da hulda tsakanin kasashe ta kawo a kasar ta Nijar, sannan kasa da watanni biyu da ziyarar da kwamishiniyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin bakin haure da kuma kwamishiniya mai kula da mutane da ke cikin tashin hankali.
Da yake magana kan wadannan yarjejeniyoyi, ministan harkokin wajen kasar ta Nijar Hassoumi Massaoudou, ya ce Tarayyar Turai dai ta kasance babbar abokiyar huldar Nijar yau shekaru da dama da suka gabata.
Ya ce "A yau kuma sabon tsari na hulda tsakanin Nijar da Tarayyar Turai ya zabi fannoni masu mahimmanci da suka hada da batun gudanar da mulki, harkokin ilimi da horo da kuma samar wa mutane ayyukan yi da duk wasu sauran ayyukan raya kasa ta hanyar tallafi kan tsarin kasafin kudin Nijar na 2021, kuma wannan sabon tsarin yarjejeniyar da ya kai na kudade CFA miliyan dubu 70 zai bamu damar kula da yankunan iyakokinmu uku da ake fama da tashe-tashen hankula a cikinsu da inganta harkokin ilimi da horo da kuma maido da muradun gwamnati ta yadda al’ummomin da ke wadannan yankuna za su ji sauki da samun walwala ta hanyar samun ababen more rayuwa kamar ko wane dan kasar ta Nijar".
Sai dai da yake magana kan wannan batu mataimaki na biyu na magajin garin karamar hukumar Tondikiwindi Honorable Oumarou Dodo Mounkaila, ya ce sannu a hankali dai sauki na samuwa.
Tuni dai suma daga na su bangaren 'yan kungiyoyin fararen hula na jihar Tillabery irin su Adamou Oumarou Mamar suka yaba wannan yarjejeniyoyi inda suka ce za su sa idanu domin ganin an kai tallafin inda ta kamata.
Abin jira a gani dai shi ne na matakin da hukumomin na Nijar za su dauka musamman ma wajen ganin al’umomin yankunan sun koma a garuruwansu ta yadda za a samu kula da su musamman a wannan lokaci da damina ke shirin sauka.