Moodys: Nijar ta gaza biyan basussukan da ta ranto
January 24, 2024Nijar ta fada cikin wannanmatsala ce saboda takunkuman da kungiyoyin ECOWAS da UEMOA suka saka wa kasar a dalilin juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata. Cibiyar binciken ta ce matsalar basussukan kasar ta Nijar na neman haddasa matsalolin kudi ga bankunan kasashen Afirka ta Yamma da dama.
Basussuka da Nijar ta gaza biya a tsawon watanni shida
Rahoton cibiyar ta Moody,s ya bayyana cewa ko a wannan wata Nijar ta kasa biyan bashin kudi miliyan 38 da dubu 700. Kuma a tsawo watanni shida bayan juyin mulki a jumulce bashin kudin da Nijar din ba ta biya ba ya kai na Dalar Amirka miliyan 485. Lamarin da cibiyar ta ce ya soma haddasa matsalar karancin kudi shiga a bankunan yankin da dama wanda kuma ke zama wata barazana ga jarinsu da ma makomarsu. To amma wasu masu adawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar na ganin ba wanda ya kamata a yi kuka da shi kan wannan matsala ta Nijar illa hukumomin mulkin sojan da suka yi juyin mulki a kasar.
Fargaban 'yan Nijar a kan wannan al'amari
wasu ‘yan Nija din dai na ganin hanya daya ta shawo kan wannan matsala ta kudi da ma sauran matsalolin Nijar ita ce hawa tebirin sulhu da kungiyar ECOWAS. Cibiyar ta Moody, s ta ce idan har aka wuce watanni shida to kuwa za a saka Nijar a jerin kasashe maras tabbas ga harkokin bashi, wadanda ba su bashi ke zama hadari.