1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi da Benin: Yarjejeniya da Nijar

Salissou Boukari LMJ
July 14, 2022

Jamhuriyar Nijar ta saka hannu kan yarjejeniyoyin tsaro tsakaninta da makwabtanta na Jamhuriyar Benin da kuma Chadi, domin yakar matsalolin rashin tsaro.

https://p.dw.com/p/4E9Mv
Nijar | Mohamed Bazoum | Shugaban Kasa | Tattaunawa da DW
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed BazoumHoto: Gazali Abdou/DW

Yarjejeniyar tsaro ta farko dai an yi ta ne da makwabciyarta kasa Benin, inda ministocin tsaron kasashen biyu suka rattaba hannu domin fuskantar lamuran tsaro na tsakanin kasashen biyu. Yarjejeniya ta baya-bayan nan ita ce tsakanin Nijar din da kasar Chadi, inda yayin ziyarar da ya kai shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum bayan karfafa huldar dangantaka ya kuma kulla wata yarjejeniya ta tsaro tsakanin Chadi da kasarsa ganin yadda kan iyakokin kasashen biyu ke bukatar kulawa daga kowane bangare. Batun kula da harkokin tsaro a Nijar lamari ne da kungiyoyin fararen hula ke biyarsa sau da kafa, inda suke bayar da shawarwari a kai. Sau tari dai kasar Nijar na shiga cikin sahun kasashe ko cikin kungiyoyi na tsaro irin na G5 Sahel ko na Majalisar Dinkin Duniya a nan cikin kasa ko kasashen waje, domin taimakawa wajen harkokin tsaro. Wannan matsala da Nijar din ta fuskanta ta tsaro a iyakokinta na Gabas da Yamma, ta sanya ta samu darussa masu yawa a fuskar tsaro. Yayin ziyarar da yakai kasar Chadin dai, shugabannin biyu na Nijar da na Chadi sun yi fatan ganin nan gaba kasar Mali ta dawo cikin tsarin G5 Sahel, wanda ake ganin zai fi samun cikakken tasiri na yaki da ta'addanci.