1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PNDS a Nijar ta fitar da dan takara

Salissou Boukari AMA
April 1, 2019

Jam’iyyar PNDS Tarayyar ta tsayar da shugabanta Bazoum Mohamed a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben 2021 da ke tafe bayan ta fuskanci rikicin cikin gida.

https://p.dw.com/p/3G1US
Außenminister der Republik Niger Mohamed Bazoum
Hoto: DW/T.Mösch

Wakillai daga jihohin kasar Nijar takwas da suka hada da kungiyar matasa da ta mata na jam’iyyar, da ma wakillan ‘yan Nijar da ke kasashe dabam-dabam na Afirka, Tarayyar Turai da Amirka ne suka tabbatar da amincewa da Bazoum a matsayin dan takararsu a zaben 2021 da ake shirin gudanarwa a kasar. 

A yanzu dai ta tabbata da Bazoum Mohamde wanda ya gaji Issoufou Mouhamadou a mukamin shugaban jam'iyyar  PNDS Tarayya ne zai tsaya takarar bayan shafe lokaci ana fuskantar cece-kuce na cikin gida kan wanda kwamitin kolin jam'iyyar mai mulki zai tsayar.

Ya ce zai ci gaba da dorawa daga inda Shugaba Issoufou Mahamadou ya tsaya wajen zartar da ayyukan gina kasar kamar karfafa manyan ma’aikatu na kasa da kuma inganta rindinonin tsaron kasar da ke fuskantar kalubalai na 'yan ta'adda, tare da kyautata fannin tattalin arziki da samar wa matasa ayyukan yi.

Kazalika batun tabarbarewar harkokin ilimi na daga cikin kalubalen da suke ci mani two a karya a matsayina na malamin makaranta In ji Mohamed Bazoum a cikin jawabinsa na rufe babban taron jam'iyyar da ya kaddamar da shi a matsayin dan takara. Bukin ya samu halartar wakilan jam'iyyun siyasa dabam-dabam na ciki da ma wajen kasar da suka hada da jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.