Tallafin jini ga mabukata a Agadez
January 15, 2019Wannan al'amari dai ya gudana a gaban hukumomin kiwon lafiya da na gwmanati da ma al'umma. Yunkurin ya zo ne a daidai lokacin da dakin adana jini na jihar Agadez ke fama da rashin ajiyayyen jini. Jinin da wadannan matasa suka bayar dai zai ceto rayukan mutane da dama da ke kwance asibitoci kuma suke fama da karancin jini. Docta Hamissou Hamidou daracta ne a ma'aikatar kula da bayarwa da kuma da ajiye jini a jihar ta Agadez, ya kuma jinjinaawa matasan da suka kawo wannan dauki.
Suma dai matsa daga karamar hukuma Agadez ba su bari an barsu a baya ba wajen yin wanan abu mai muhimanci, domin kuwa suna daga cikin matasan da suka bayar da gudunmawar jinin. A nasa bangar4en daractan ma'aikatar kiwon lafiya a jihar ta Agadez, Chaibou Yami Mamadou ya jinjinawa matasan tare kuma da yin kira ga sauran kungiyoyi na matasa da su bi sahunsu.