Sojan Chadi za su halrci yakin ta'addanci
March 11, 2021Bikin da ya wakana a karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Alhaji Mahamadou Issoufou da kuma shugaban kasar ta Chadi Marechal idriss Deby Itno a yayin jawabi a gaban sojojin ministan tsaron kasar Nijar Farfesa Issoufou Katambe ya bayyana tasirin da ke tattare da zuwan sojojin Chadi game da batun zaman lafiya "Shugabannin kasashen da suka hallara a nan, sun zo ne su ga halin da kuke ciki , tanadin da aka yi maku kafin dagawarku zuwa fagen daga inda za ku hadu da sauran takwarorinku na kasashen Mali Nijar da Burkina Faso na rundunar hadin gwiwa domin yin aiki kafada da kafada. Kuma muna da tabbacin cewa za mu samu sakamakon mai kyau a cikin aikin."
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya kasance farin wata sha kallo a wajen wannan biki, kana takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou ya yaba da irin rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel, kafin daga karshe ya bashi lambar girmamawa mafi girma ta kasar Nijar. Ko baya ga shugaba Deby , Shugaba Mahamadou Issoufou ya kuma bayar da irin wannan lambar girma ta Nijar ga Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a game da abin da ya kira rawar da yake takawa wajen samar da zaman lafiya tsaro da ci gaba a yankin sahel. Faransa ce ta dauki nauyin zuwan sojojin Chadin a yankin na Tera da ke yammacin Nijar iyaka da Burkina Faso da Mali, kana masu sharhi kamar Moussa Akasar mai dan jarida mai binciken kokof kana mai sharhi kan harkokin tsaro a Nijar ya dalilin na ganin Faransa na daukar nauyin sojojin Chadin ne a kokarin da take na janye sojojinta daga yankin.