1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Baraka ta kunno kai a jam'iyyar Lumana

Salissou Boukari
March 21, 2019

Sabon rikici ya kunno kai a cikin babbar jam’iyyar adawa ta Lumana Afrika ta Hama Amadou inda shugaban riko na Jam’iyyar Oumarou Noma ya fitar da takardar dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar

https://p.dw.com/p/3FRMb
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Wadannan mutane dai sun hada da Honorable Soumana Sanda dan majalisar dokoki, da tsohon magajin garin da'irar birnin Yamai Oumarou Dogari, da Youba Diallo, da Salissou Leger Maradi, da kuma wanda ake kira Algerien Inda ake tuhumarsu da take dokokin jam'iyya.

Tun dai da jimawa ake rade-radin wannan rigima da ta Jima tana wanzuwa a cikin jam'iyyar ta Lumana Afrika musamman ma waren jagorancin jam'iyyar reshen birnin Yamai da ma batun fitar da dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Inda duk da cewa jam'iyyar ta jima da tabbatar da Hama Amadou shugaban jam'iyyar mai gudun hijira a matsayin wanda zai tsayawa jam'iyyar takara, amma wasu ke ganin cewa tamkar batawa jam'iyyar lokaci ne ganin babu yadda za a yi Hamma Amadou ya yi takara a wannan lokaci sakamakon hukumcin da yake kanshi na dauri na kiminin shekara guda a gidan yari sakamakon tsohon batın nan na safarar jarirrai.

A halin yanzu dai wadanda aka bada sanarwar an fidda daga cikin jam'iyyar sun ce, su basu da abin cewa a halin yanzu, yayın daga bangaren uwar jam'iyyar ata bakin Sakatarenta suka ce wannan ba wani sabon abu ba ne rikici ne na cikin gida kuma wadanda ake batın a kansu ‘yan jam'iyya ne kamar ko wanne.

Don haka su basu ga abun managa ba a nan. Tuni dai magoya bayan jam'iyyar musamman ma bangaran wadanda aka dakatar din suka nuna cewa wannan batu tamkar magana ce da ake kira shaci fadi, domin batu ne da ba zasu taba yarda da shi.