Ba ta sauya ba a kan iyakokin Nijar
February 26, 2024Bayan da shugabannin kasashe mambobin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO suka sanar da janye wani bangare na takunkumin da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, wwadanda suka hadar da bude kan iyakokin kasashe mambobin kungiyar da ke makwabta da Nijar 'yan kasar mazauna kan iyakokin Bénin Nijar din da kuma Najeriya suka shiga nuna murnarsu. To sai dai kwana biyu da wannan sanarwar babu wani sauyi a kan iyakokin, hasali ma dai dakarun sojojin Nijar da aka jibge a kan iyakokin na cikin shirin ko ta kwana. Daga bangaren gwamnatin kasar Nijar kuwa, har kawo yanzu ba su ce uffan ba.
Moussa Amadou Modibo wani mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum, ya ce dole ne gwamnatin kasar ta yi taka-tsan-tsan da makwabtan nata na Benin da Najeriya. Hadiza wata 'yar kasuwa a tashar jirgin ruwa ta ce, fatan 'yan kasuwa shi ne shugabannin su yi iyakar bakin kokarinsu domin ganin an samu jituwa a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna. A ra'ayin Attiku Dotti wani mai sharhin kuwa, har yanzu da sauran rina a kaba idan har za a sasanta matsalar da ke tsakanin ECOWAS ko CEDEAO da kuma Jamhuriyar Nijar. Shi kuwa dan kasuwa Elhadj Issifou Hayyatou cewa ya yi, akwai bukatar gwamnatin Nijar din ta dubi talakawa da idon rahama. 'Yan kasa dai na ci gaba da zurawa gwamnati idanu, domin ganin irin matakin da za ta dauka a tsakanin bude nata iyakokin ko kuma ci gaba da rufe su.