Nijar: Ana jiran sakamakon zaben shugaban kasa
February 21, 2021Wasu jami'ai bakwai na hukumar zabe mai zaman kanta (Céni) a Nijar sun mutu bayan da motarsu da ta bi ta kan nakiya a yankin Tillabéri na yammacin kasar kusa da Mali. Gwamnan yankin Tidjani Ibrahim Katiella, ya bayyana cewar hatsarin ya raunatar "Mutum uku". Mutuwar wadannan mutane bakwai ta zo ne a yayin da ake kammala zagaye na biyu na zaben shugaban kasa tsakanin Mohammed Bazoum na bangaren masu mulki da Mahamane Ousmane, tsohon shugaban kasar na bangaren adawa.
Wannan bala'in ya faru ne a kauyen Waraou, da ke cikin yankin Dargol a yankin Tillabéri mai nisan kilomita dari daga Yamai babban birnin kasar. Kamar dai yadda dokar tsarin zaben ta tanada kusan illahirin runfunan zabe sun rufe da karfe bakwai na yamma. Sai dai a wannan zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a birnin Yamai Jama’a ba su fito ba kamar yadda aka gani a zagayen farkon na zaben shugaban kasar a cewar Eli bossoma na kungiyar masu sa ido ta CADDHR ya shaida.
Hukumar zaben Nijar ta bayyana gamsuwarta da yadda zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali a kusan duk fadin kasar. Amma kuma mai shari’a Aladoua Amada mataimakin shugaban hukumar zaben ta CENI ya bayyana cewa jami’ai sun yi nasarar kama wasu mutanen da suka yi yunkurin tafka magudi a zaben ta hanyar shigo da takardun zabe na jabu daga wata makwabciyar kasar.
A yankin Agadez da ke arewacin kasar rahotanni sun ce an yi zaben cikin kwanciyar hankali, ganin yada tsarin zaben da ma yada aka dauki kwararan matakai na tsaro, sai dai wasu 'yan Nijar sun kasa samun zarafin kada kuri'a, haka zaben ya gudana a yankin Tahoua, inda aka tabbatar da gudanar da zabden a cikin tsanaki. A birnin Maradi da ke zama cibiyar kasuwancin Nijar, an bude rumfunan zabe cikin lokaci, duk da 'yan kurakuran da aka samu, zaben ya gudana a cikin natsuwa. Mata da matasa dai sun fito da himma wurin wannan zabe kuma cikin ladabi da biyayya wanda hakan ya tabbatar da amsa kiran masu jan hankalin jama'a.