1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon ambaliyar ruwan sama a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari
October 24, 2016

Daga watan Yuni zuwa watan Oktoba, ofishin kula da wadanda ke cikin hadari na Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ya sanar cewar mutane akalla 50 sun mutu wasu dubbai sun rasa matsugunnansu a Nijar.

https://p.dw.com/p/2RchF
Niger Zerstörung nach Flut
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Ambaliyar ruwan sama da aka samu a Jamhuriyar Nijar daga watan Yuni kawo yanzu, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 50, yayin da wasu mutanen dubu 123 suka rasa gidajensu a wani adadi na baya-bayan nan da ofishin Majalisar Dinkin Duniya na OCHA ya fitar, kuma hakan ya shafi musamman ma yankunan da suke na Sahara ne.

A tsakiyar watan Agusta dai wani adadin da gwamnatin kasar ta Nijar ya bayar ya ce mutane 14 ne suka rasu yayin da wasu dubu 46 suka rasa gidajensu. Sai dai a cewar Majalisar Dinkin Duniya da ma Gwamnatin ta Nijar, kashi uku cikin hudu na wannan adadi an sameshi ne a yankunan Maradi, Tahoua da kuma Agadez.