1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Netanyahu ya kai wa sojojin Isra'ila ziyara a Gaza

July 18, 2024

Ziyarar Netanyahu ta zo ne a lokacin da ya ke shirye-shiryen yin jawabi ga majalisar wakilan Amurka kan yakin Gaza.

https://p.dw.com/p/4iUFw
Benjamin Netanyahu a birnin Rafah
Benjamin Netanyahu a birnin RafahHoto: Avi Ohayon/Israel Prime Minister's Office/AP/picture alliance

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kai wa dakarun sojin kasar dake fagen daga ziyarar ba-zata a kudancin Gaza a ranar Alhamis.

Yayin ziyarar Netanyahu ya ce kasancewar zirin da ke kusanci da Masar karkashin ikon Isra'ila abu ne mai matukar muhimmanci.

Wannan na zuwa ne yayin da firaiministan ya ke shirye-shiryen yin jawabi ga majalisar wakilan Amurka.

Karin bayani:Gangami adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu

A kalaman da ya yi a birnin Rafah, Netanyahu ya nuna alamun nasara akan Hamas, ya kara da cewa akwai sauran aiki a gaba kafun akai ga tsagaita wuta da aka shafe watanni ana nema.

Karin bayani: Netanyahu na fuskantar matsin lamba kan yakin Gaza

Tun a ranar bakwai ga watan Oktoban shekarar 2023 aka fara yaki tsakanin Isra'ila da Hamas lamarin da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiya musamman a zirin Gaza.