Netanyahu: Dole a kwance damarar mayakan Hamas
October 3, 2017Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta yi fatali da ko wane shirin sulhu tsakanin manyan kungiyoyi biyu na Falasdinawa har sai an kwance damarar mayakan kungiyar Hamas mai samun goyon bayan kasar Iran.
Netayanhu ya fada a cikin wata sanarwa cewa Isra'ila ba ta da shirin amincewa da duk wani shirin sulhu wanda wani bangare na Falasdinawa zai yi sulhu da wani bangare da ke barazana ga wanzuwar Isra'ila.
Ya ce duk mai son yin wannan sulhu dole ne ya amince da kasar Isra'ila, ya kwance damar mayakan Hamas kana kuma ya katse huldar dangantakarta da kasar Iran mai kira da a ruguza Isra'ila.
Hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinu da duniya ta amince da ita ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila amma Hamas da ke mulki a Gaza wadda kuma tun a 2008 ta gwabza yaki har sau uku da Isra'ila, ta ki amincewa da wanzuwar Isra'ila.
A kwanan nan dai kungiyoyin Fatah da Hamas sun kusanci juna a kokarin yin sulhu tsakaninsu bisa jagorancin kasar Masar.