1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Navalny: NATO ta bukaci daukar mataki

Abdullahi Tanko Bala
September 4, 2020

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta yi kiran gudanar da bincike na kasa da kasa game da gubar da aka sanya wa jagoran adawa na kasar Rasha Alexei Navalny.

https://p.dw.com/p/3i10Z
NATO Generalsekretär  Jens Stoltenberg
Hoto: Getty Images/AFP/K. Tribouillard

Kungiyar ta NATO ta kuma bukaci Rasha ta yi wa hukumar yaki da makamai masu guba cikakken bayani kan shirinta na gubar Novichok.

Shugaban kungiyar kawancen tsaron ta NATO Jens Stoltenberg bayan wani taron gaggawa da mambobin kasashen kawancen suka yi kan gubar da aka sanya wa Navalny yace wajibi ne Rasha ta bada cikakken hadin kai ga masu binciken.

Yace wannan ba wai hari ne aka kai akan mutum guda ba amma hari ne akan yancin dimukuradiyya kuma ya saba dokokin kasa da kasa.

Tun da farko gwamnatin Jamus ta sanar da cewa gubar da aka sanya wa Navalny wani nau'i ne na Novichok da sojoji ke amfani da shi a matsayin makamin yaki wanda ya yi daidai da abin da hukumomin Birtaniya suka ce an sanya wa wani dan leken asiri Sergei Skripal a shekarar 2018 wanda shi ma aka dora alhakinsa akan Rasha.