NATO za ta ci gaba da ba Ukraine makamai
June 15, 2023Talla
Kasashe da dama na kungiyar ta NATO sun yi alkawarin samar da sabbin makamai da kuma ci gaba da taimaka wa Ukraine da makamai.
Sakataren kungiyar kawancen tsaron Jens Stoltenberg ya ce taimakon da NATO ke bai wa Ukraine na yin tasiri a fagen yaki
A nasa bangaren sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce Ukraine na bukatar taimako na gajeren zango da kuma na dogon zango.
Kasashen Denmark da Netherlands da Burtaniya da Amurka sun sanar da yunkurin hadin gwiwa na bai wa Ukraine makamai kirar tarayyar Soviet na kakkabo jiragen sama.