1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya soki Jamus kan bai wa Rasha goyon baya

Yusuf Bala Nayaya
July 11, 2018

Gabanin soma taron shugabanin kungiyar tsaron NATO a birnin Brussels, shugaba Trump ya zargi Jamus da son marawa Rasha baya saboda wani shiri na fadada bututun samar da iskar gas da ke a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/31HNh
Belgien Nato-Gipfel
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Trump bayan ya soki Jamus da sauran takwarorinta kan rashin kara kudade da suke kashewa harkokin tsaro a yayin jawabinsa ga manema labarai, a bangare guda, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce babu adalci a ce Amirka na biyan makudan kudade don ba da kariya ga kasashen Turai yayin da kasa kamar Jamus da tafi karfin tattalin arziki a Turai  na tallafawa yarjejeniyar kasuwancin iskar gas da Moscow. Jamus ta kasance karkashin sasari na Rasha a cewar Trump.

Belgien Nato-Gipfel
Ministar tsaron Jamus Ursula von der LeyenHoto: Reuters/R. Krause

Ita ko ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen da ta mayar da nata martanin ga kalaman na Trump, ta ce ta gaza fahimtar me shugaban na Amirka ke nufi da wadannan kalamai cewa "ana juya kasar ko ma an sa mata sasari". yayin da a bangare guda suke da batutuwa da dama da suke ci gaba da tattaunawa da Rasha?

Trump dai ya sha fadin cewa kasashen Turai da Kanada na tafiyar hawainiya wajen kashe kashi biyu cikin dari na abin da ke shigarwa kasashen a fannin na soja. A cewar Trump tsawon shekaru kama daga goma zuwa ashirin Amirka ta kasance me bin bashi ga sauran kasashe mambobi na NATO kan abin da suke kashewa ta fiskar tsaro.