1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta bayyana kalaman shugaba Putin da cewa ba zasu taimaka ba

June 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuJo

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi suka ga martanin baya-bayan nan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya mayar game da shirin Amirka na kera makaman kandagarkin harin makaman nukiliya. NATO ta bayyana kalaman na Putin, wadanda suka zo gabanin taron kolin kungiyar G8 da cewa ba zasu taimaka ba. A cikin wata hira shugaba Putin yayi kashedin cewa Rasha ka iya komawa ga matsayinta na lokacin yakin cacar baka, idan gwamnati a Washington ta ci-gaba da shirinta na kakkafa sansanonin kandagarkin makamai masu linzami a kasashen Poland da Czeck. Putin ya ce shirin wata barazana ce da ka iya maido da tserereniyar kera makamai a Turai. Ya ce ba za´a iya ganin laifin gwamnati a Mosko ba domin Washington ce ta fara wannan shiri. Amirka ta ce shirin ta na da nufin kare ta daga duk wani harin makami mai linzami daga kasashe kamar Iran da KTA.