1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar tsaro ta NATO za ta yi taro kan Rasha

Abdoulaye Mamane Amadou
September 6, 2020

Kungiyar tsaro ta NATO za ta gudanar da taron cimma matsaya kan matakan da suka cancanta ga kasar Rasha wacce ake zargin hukumominta da laifin saka wa madugun 'yan adawar Alexeï Navalny guba.

https://p.dw.com/p/3hyvf
Deutschland Berlin | Krankenhaus Charité | Behandlung Alexej Nawalny
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Sommer

A nata bangare ita ma kungiyar tarayyar Turai ta ce akwai yiwuwar ta dauki wasu kwararan matakan ladabtarwa ga kasar Rasha, inda babban jami'in huldar diflomasiyarta Josep Borrell, ya bukaci hukumomin Moscow da su bayar da hadin kai tare da kaddamar da cikakken bincike.

A ranar 22 ga watan jiya ne aka kwantar da madugun 'yan adawar ta Rasha Alexeï Navalny a wani asibintin soja da ke Berlin na nan Jamus, kana daga bisani wani binciken kwararru ya tabbatar da cewa ya shaki guba ce mai sarke jijiyoyi da ake kira  Novitchok.