NATO: Cigaba da yaki da ta'addanci
September 11, 2021Talla
Jens Stoltenberg ya sha wannan alwashin ne yayin nuna ban girma ga wadanda harin ta'addancin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 ya rutsa da su a cibiyar kasuwancin ta duniya da ke Amirka.
Yayin bikin tunawa da ranar a Hedikwatar kungiyar da ke birnin Brussels fadar gwamnatin kasar Beljium, Stoltenberg ya ce kungiyar zata cigaba da taka rawar da ta ke yi a yaki da ta'addanci.
A yayin bikin an yi kasa-kasa da tutocin kawance 30 don karrama kimanin mutum dubu uku da suka mutu a harin da Al-Qaeda ta kai, hari mafi muni a tarihin Amirka. Amirka da kawancen NATO dai sun mamaye Afganistan bayan harin a wancan lokacin, tare da kwace ikon kasar a hannun kungiyar Taliban da ke da tsattsaurar ra'ayin addinin Islama.