Kungiyar tsaro ta Nato zata gudanar da taro a Brussels
December 4, 2018Talla
A watan Maris din wannan shekara ne Rasha ta kaddamar da wani sabon makami mai linzami mai lakabin Novator al'amarin da Amirka ta baiyana da karya ka'ida tare da yin barazanar ficewa daga kungiyar tsaron, kodayake har ya zuwa wannan lokaci Rasha na kare kanta daga zargin karya ka'idodin makamai da kungiyar tsaron tayi tanadi tun a shekara ta 1987.
Yayin taron dai ana sa rai ministocin harkokin wajen kungiyar da yawansu yakai 29 zasu tabo batun rikicin daya kunno kai tsakanin Rasha da Ukraine bayan da Rasha ta kame jiragen ruwan kasar ta Ukraine bisa zargin su da wuce iyaka.