Rasha ta kare kanta game da makamai masu Linzami
November 1, 2018Talla
Wannan kira na zuwa ne yayin ganawar jakadun kungiyar tsaro ta NATO da takwaransu na kasar Rasha a ranar Laraba bayan babban sakataren kungiyar tsaron ya bayyana yadda kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Rasha ta karya dokar da ta haramta mallakar nau'in wasu makamai masu linzami tsakanin kasashen kawance, lamarin da ya ce na zaman barazana ga wasu kasashen Tarayyar Turai.
A nata bangaren Rasha ta baiyana cewar ko kadan mallakar wadannan sabbin makamai masu linzami bai ci karo da dokar da kungiyar tsaron ta yi tanadi tun a shekara ta 1987 ba.