Nasara kan 'yan fashi a Arewacin Najeriya
July 21, 2015
A wani matakin da gwamnonin jihohin Arewa guda shida suka dauka na magance tsanantar ayyukan 'yan fashi da makami da ke sace garkunan shanu da 'yan ta'addan da ke boyewa cikin dazuzzukan Arewacin kasar suna cutar da alumma, Yanzu haka dai gwamnonin da ke da makwabtaka da juna, sun bawa dakarun sojojin Najeriya damar shiga cikin dazuzzukan yankunan, domin kawar da 'yan fashi da makami da 'yan ta'addan da ke zaune a cikin dokar daji.
Hadakar dakarun tsaran Najeriya da suka kaddamar da wannan atisayi kimanin mako daya kenan, sun sami damar hallaka 'yan fashi da 'yan ta'adda da damar gaske da ke zama a cikin dokar dajin jihar Sokoto da Kebbi da Katsina da Kaduna da Niger da Zamfara.
A rangadin da Gwamna Nasiru el-Rufa'i ya kai a cikin dajin karamar hukumar Birnin Gwari a kaduna, ya nuna jin dadinsa ga irin nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu, inda ya ce sojojin zasu ci gaba da aiki har sai a kawar da wadannan 'yan fashi da ma wasu masu miyagun laifuka a dazukan.