Kebbi: Ceto yaran da aka sace zuwa kudu
October 2, 2024Kananan yaran su 19 da gwamnatin Kebbin ta kubutar, bayan nasarar yin wani aikin hadaka tare da samun bayanan sirri tsakanin hukumomin jihar da na hukumar ta NAPTIP. Yaran dai an sace su ne daga Kebbin, aka kuma nausa da su zuwa jihar Cross River da ke kudancin Najeriyar. Hadin kan da Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Najeriyar ta ce ta samu daga hukumomin jihar Kebbi ya taimaka matuka, wajen tsara samamen da suka kai dangane da kubutar da wadannan yaran a jihar ta Cross River. Tuni dai kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkokin mata da kananan yara suka rufa baya, tare da kiraye-kiraye na ganin an hukunta wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a safarar wadannan yara tare da cin zarafinsu. Wannan dai kusan ba shi ne karon farko da ake ceto yara, wadanda aka sace daga jihar aka kai wasu jihohin kudancin kasar ba.