1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Za mu magance rikicin Boko Haram

Abdullahi Tanko Bala
December 15, 2018

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi sun yi wata ganawa a Najeriya domin karfafa kudirinsu na yaki da Boko Haram a cewar fadar gwamnatin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3ACI0
Nigeria Tschadsee Konferenz
Hoto: State House, Abuja

Taron kolin wanda ya hada da kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da Niger da Benin da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, tishi ne akan taron da shugabannin suka gudanar a watan Nuwamba a birnin Njdamena na kasar Chadi domin shawo kan karuwar hare haren Boko Haram a yankunan da ke fama da tashe tashe hankula.

A jawabinsa na bude taron shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace kasashen sun nuna kudiri mai karfi yakar abokan gabar su na bai daya musamman kan karuwar hare hare akan sojoji da kuma yawaitar satar mutane akan iyakoki domin neman kudin fansa.

Shugabannin kasashen sun kuma yi roko ga al'umomin yankunan su bada hadin kai wajen bayar da bayanai da za su taimaka wa jami'an tsaro domin kawo karshen tashin hankalin.