1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Za a ci gaba da sayan mai a kan Naira 162.5

January 25, 2022

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da dakatar da zare tallafin man fetur har na tsawon akalla watanni 18 da ke tafe. A ka'idar dokar man fetur dai ,daga 16 ga watan Fabrairu ne ya kamata ta dakatar da tallafin man fetur.

https://p.dw.com/p/4646G
Gidan mai a Legas
Wata ma’aikaciya na cika tankar mai a gidan mai da ke kan wani titi a Legas a NajeriyaHoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Wani rikici na 'yan kodago da kila ma jama'ar cikin gari ya tilasta ma gwamnatin Najeriya sauya rawa  tare da dakatar da zare tallafin man fetur har na tsawon wasu watanni 18 dake tafe. Karamin ministan man fetur na tarrayar Najeriya ya ce tun daga wannan mako har ya zuwa wata na yulin dake tafe ne dai  al'ummar kasar za su ci-gaba da biyan Naira 162.5 a matsayin farashin kowace litar man, duk da korafin 'yan mulki a matakai daban-daban cikin kasar.

Wajen wani taro na manema labarai dai Timpre Silva ya ce gwamnatin na shirin tabbatar da aikin matatan mai na kasar da ma wasu jerin matakan da ke rage radadin zare tallafin man fetur.

Man fetur a jarkoki
'Yan Najeriya sun saba jiran cika jarkoki a yayin matsalar karancin man feturHoto: picture-alliance/ dpa

Ya ce "Mun yi alkawarin sake fasalin motoci akalla miliyan daya domin komawa aiki da iskar gas da kuma samar da gidajen da za su sai da iskar gas din. Mun yi nisa kan wannan, kuma sai mun kai nan kafin mu fara tunanin zare tallafin. Haka kuma muna tunanin samar da tallafi, ministar kudi ta ayyana niyyar taimaka wa al'umma. Duk wadannan sai sun hadu kafin mu sanar da zare tallafi. Saboda shugaban kasa ba ya son ganin 'yan kasa na wahala. ”

Majiyoyi sun ce  gwamnatin Najeriyar na shirin tura batun na tallafi ya zuwa ga gwamnatin da ke shirin zuwa a nan gaba da nufin kauce wa jefa kasar cikin rikicin da ke iya shafar daukacin makoma na kasar. 

Tuni dai 'yan kodagon kasar suka shirya wata zanga-zanga a daukacin jihohi na kasar da Abuja daga Alhamis  da nufin nuna bacin ransu bisa matakin kafin sabuwar sanarwar 'yan mulkin. Amma Ayuba Wabba da ke zaman shugaban kungiyar kodagon kasar ta NLC ya ce sun mai da wuka kube bayan nasarar da suka ce sun samu na tilasa wa Abujar komawa lungu.

Nigeria | Jerin matsaloli | Zanen barkwanci
Cire tallafin man fetur na iya yin tasiri a siyasar NajeriyaHoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

Ana kallon sabon matakin da ruwa da tsaki da bakin hadari na siyasa da kila guguwa mai karfi da ke iya shafar daukacin kasar ta Najeriya a halin yanzu. Ko bayan 'yan kodagon kasar dai akwai tsoron yiwuwar fita cikin gari a bangaren talakawa da da kyar da gumin goshi suka koma cikin gida bayan zare tallafi na tsohuwar gwamnatin kasar shekaru 10 da suka gabata.

Zare tallafin man fetur din na iya shafar farin jinin jam'iyyare APC mai mulki da ke shirin sake komawa zabe nan da shekara guda kacal. Sai dai a fadar Faruk Ahmed da ke zaman babban sakatare na hukumar kula da hajar man fetur ta kasar, babu batun siyasa a cikin hukunci na gwamnatin kasar bisa makomar tallafin.

" Lita miliyan sittin da biyar ne dai tarayar Najeriyar ta ce tana ta kwankwada a kusan kullum a cikin batun tallafin da mafi yawansa ke karewa a cikin fasakwauri ya zuwa kasashe na makwabta domin neman riba.