1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yunkurin dawo da kudaden da aka sace

October 27, 2017

Bayan daukar dogon lokaci ana fafutika, gwamnatin Tarrayar Najeriya ta fara ganin alamun haske a kokarinta na dawo da dubban miliyoyin daloli da 'yan kasar suka kwashe suka tura kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/2mdmX
Zentralbank von Nigeria
Cibiyar babban bankin Tarayyar Najeriya na CBN da ke birnin Abuja

Najeriya dai ta dauki lokaci tana yakin neman dawo da kudade da wasu 'yan kasar suka kwasa suka jibge a kasashen waje. To sai  dai kuma sai yanzu ta fara ganin alamun haske tare da wata kotun birnin Ingila da ta bada umarnin mika mata tsabar kudi har dalar Amirka Miliyan 85 da ya ce mallaki ne na 'yan Najeriya. Wannan ne dai karo na farko da kasar ke karbar wani sashe na kudade na haramun tun bayan kaddamar da sabon yaki da cin hancin na gwamnatin 'yan sauyi ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Nigeria Geldwechsler
Hotuna na kudadan Najeriya da ake tantancewa da na'urar tantance kudadeHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da cewar dai kasar ta yi nasarar alkawari da kasashe na duniya da daman gaske, jan kafa na zaman karatu na kasashen game da batu na kudaden abun kuma da ke nuna alamun sanyin gwiwa ga kasar. Ana dai kallon sabon matakin a wani abun da ke iya karfafa gwiwa ga kasar da ke da bukatar kudadenta  da ke kasashen waje amma kuma ke fuskantar tarnaki a halin yanzu.

Batun yaki da hancin dai na zaman daya a cikin alkawura guda uku da gwamnatin 'yan sauyi ke tunkaho da shi a tsakaninta da al'ummar kasar. Kuma mafi yawa na kusan dalar Amurka Miliyan dubu dari hudun da ake fadin an sace, na a kasashen waje, abun kuma da ya sa dawowa da kudin ke iya bude sabon babi ga kasar da ke da matukar bukata a yanzu. Tuni dai  batun dawo da kudaden ya fara daukan hankalin 'yan kasar da ke masa kallo na lalle da maharbin. Abun jira a gani dai na zaman nisa na hadin kai a tsakanin kasashen na waje da ke da fatan ganin sauyi a Tarrayar Najeriyar da ta yi alkawarin yaki da hanci a ciki na tsakani da  Allah.