1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria: Yan shi'a sun yi bikin ranar Kudus

Usman Shehu Usman
June 23, 2017

'Yan sanda a Kaduna sun yi amfani da karfi don tarwatsa masu mabiya Shia'a da suka fito gudanar da bikin ranar da suke tunawa da korar Falasdinawa daga birnin Kudus

https://p.dw.com/p/2fIcT
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Rahotonni da DW tattara sun bayyana cewa, mutane da dama aka jikkata yayin da jerin gwanon Shi'a a Kaduna, inda 'yan sanda suka yi amfani da hayki mai sa kwalla kan 'yan Shi'ar. Wakilin DW Ibrahima Yakubu, ya shaida mana cewa da farko zauna gari banza na gungun matasan cikin gari, su ne suka fara yin fito na fito da 'yan Shia'a, inda su kuwa jami'an tsaro suka shiga rikicin, suka fara tarwatsa 'yan Shi'ar. 

Sai dai sabanin aikin tsaro da ya kai yan sanda, sun buge da tarwatsa zanga-zanaga, kana suka yi ta kama mutane ciki har da kananan yara da 'yan jarida. Wakilin DW da ke cikin yan jarida wadanda aka kama duk da cewa ya nunawa yan sandan katin shaidarsa na aiki, suka yi awon gaba da shi suka lalata masa kayan aiki, suka kuma lakada masa duka. Yanzu dai an sako wakilin na DW bayan da kungiyar yan jaridu reshen Jihar Kadunan NUJ ta sa baki,